Rahotanni sun ce an kai hari ne a masallacin Imam Sadiq da ke lardin gabashin birnin kasar a lokacin da mutane ke shirin fara Sallar Juma'a.
Ana dai ci gaba da samun karuwar adadin wadanda harin ya rutsa da su har yanzu kuma Karon farko ke nan da aka kai irin wannan harin a masallacin jumma’a na ‘yan Shia a Kuwait.
Kungiyar IS da ke da reshenta da Lardin Najd ta yi ikirarin kai wannan harin karkashin jagoranci wani shugabanta Abu Suleiman al-Muwahhid.
Tuni dai kasashen Duniya suka fara allawadai da wannan harin, tare da alkawarin hadin kai domin daukar fansa akan ayyukan ta’adanci.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan, mai magana da yawun Kungiyar IS Abu Muhammad al Adnani ya bukaci al’ummar Musulmi su kaddamar da Jihadi domin mutuwar shahada a cikin watan Azumin Ramadan mai alfarma.288